Yaki da shan miyagun kwayoyi a jihar Sokoto
August 12, 2025Ranar 12 ga watan Agustan kowace shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar tunawa da matasa ta duniya da nufin duba ci gaban da matasan ke samu ko akasin hakan a fadin duniya.
A Najeriya, kimanin kaso 70 cikin dari na al'ummarta matasa ne, hakan na nuni da cewa akwai bukatar kulawa ta musamman ga wannan yankin na al'umma. Matasa a jihar Sokoto na fuskantar manyan kalubale na karancin ilimi da rashin aikin yi wanda matasan ne da kansu ke kokarin cire wa kansu kitse a wuta. Ambasada Yakubu Abubakar shi ne shugaban kungiyar matasa ta kasa reshen jihar Sokoto.
"Zaman mu matasa mun fi bada gudunmuwa wajen wayar da kai da kuma karkato da hankullan matasa da su nemi sana'a da ilimi, sai a a samu ci gaba bakin gwargwado. A koya masu sana'oi yau da gobe maza da mata. ina kira ga shugabanni su kara daukar matasa da muhimmancin.”
Wani al'amari da ke kawo tarnaki wajen ci gaban matasan a jihar Sokoto ba ya rasa nasaba da shiga harkokin bangar siyasa ba, wanda Dr. Ibrahim Baba Shatambaya da shima ke jibintar harkokin matasa ya ce abin na kara munana.
"Jahar Sokoto kamar yadda muke gani a wasu jihohin arewa matsalar mai girma ce, duba da cewa ba maza ne ba kawai ke yi ba, mata da yawa suna shiga. Abin da ya sa abin ya girmama shine yan siyasa wadanda ke rike da madafun iko da kuma masu kokarin ganin kansu a madafun iko su ne ke taka gagarumar rawa wajen ingiza wadannan kuma gwamnati ba ta taka gagarumar rawa wajen ganin wannnan matsalar an dauketa ba.”
Wani reshe na kungiyoyin matasan a Sokoto da ya dukufa wajen ganin rayuwar matasa ta ingata sun ce tuni suka fara ganin tasirin abinda suke yi ga wasu matasan inji Dr. Nuradeen Muhammed na kungiyar Sokoto Professionals Network.
"Akwai hanyoyi da dama wadanda muke bi wajen taimaka wa matasa, wadannan hanyoyin sun hada da basu horon sana'oi.”
Malam Abubakar Yakubu wani matshi ne da kokarin kungiyoyin matasan ya ceto rayuwarsa biyo bayan rashin abin yi duk da cewa ya kamala karatun jami'a.
"Bayan na samu horasawa sai ban kwanta ba, ilimin da na samu sai na bashi muhimmanci sama da wanda na samu a jami'a wajen sama wa kaina aikin solar, idan kana sa solar in abubuwa suka ci gaba zaka fara saida kayan solar, har kuma abubuwa su ci gaba kaima ka bude kamfaninka.”