Matakin yaki da cin hanci a Najeriya
February 6, 2025
Hukumar ta ICPC mai zaman kanta da aka kafa a shekara ta 2000, ta ce aikin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, aiki ne mai cike da kalubale na ha maza ha mata,bisa laakkari da yadda masu taadar ta cin hanci da rashawar, basu da alamun zasu saurara balle su daina.
Hukumar ta kara cewar, salo salon cin hanci da rashawar, musamman a tsakankanin manya da kananan jamian gwamnati na da yawa, da suka hada da ko dai a yi zulaken kudaden kwangila, ko kuma a yi ta maimata biyan kudin kwangilar aiki daya tilo sau shurin masaki, ba kuma tare da an ga aikin a kasa ba.
Karin Bayani: Ko za a iya magance cin-hanci a Najeriya?
Matsalar dai ta cin hanci a Najeriyar, matsala ce da ta yi katutu a tsukin Yan kasar, da kuma ke bukatar tallafin kowa domin shawo kan ta, ta yadda zaa fara ganin ci gaba a ayyukan raya kasa inji ICPC.
ICPC din dai ta nunar cewar a yanzu ta fara aikin hada hannu da karfe da wasu kasashen Afirka, don tunkarar aikin ganowar kudin haram da masu halayyar ta cin hanci da rashawa suka sace daga nahiyar suka kai boyo a Turai da Amurka.
Akwai dai misalin manyan ayyukan kwangiloli 1500 da ICPC din ta ce ta gano an bada su a sassan Najeriyar da ke cike da zulaken kudi har na naira biliyan 29.7, wadda kuma ta kwato su. Ta kuma ce kawo yanzu ta karfi korafe korafen jamaar Najeriya kimanin 851,inda ta bincika 95 daga ciki, tare kuma da mika 72 gaban kotu.
Alkaluma dai sun nuna cewar Najeriya da ke ta 120 cikin kasaashen duniya 140 da kurar su ta yi kuka kan katutun cin hanci da rasahawa, ta rasa kimanin Dala biliyan 550 ga Yan cin hanci da rashawa da ke kasar cikin shekaru 60 tun bayan samun Yancin kai .
Ko da EFCC ma sai da ta nunar ta kwato kudin haram daga hannun jama'a har Dala miliyan 750 a shekarar 2021. Najeriya dai ,kan rasa Dala bliyan 18 a duk shekara sakamakon cin hanci da rashawa.
Na yi ta kokarin jin ta bakin shugaban hukumar ta ICPC ta kasa Musa Aliyu, sai dai ta Text da ya turo min,ya ce yana kan ganawa da jamian hukumar tasa ta ICPC.