Burodi na neman gagarar 'yan Najeriya
July 21, 2022A Larabar wannan makon ne dai uwar kungiyar ta kasa ta bayar da umarnin shiga yajin aikin, kuma tuni 'ya'yan kungiyar suka amsa wannan kira. Ga misali a jihohin Katsina da Lagos, wakilan DW Hausa sun ruwaito cewa tuni yajin aikin masu gidajen burodin ya kankama. Tsadar kayayyaki dai na saka a kara kudin burodin, yayin da a hannun guda al'umma ke ganin laifin masu- gidajen burodin. Wannan dai na daga cikin dalilan masu sana'ar gasa burodin na shiga yajin aiki, domin ganin mahukuntan kasar sun yi abin da ya kamata. Wadanda ke sayen burodin yau da kullum musamman masu iyali, na ci gaba da bayyana damuwarsu kan yadda suka wayi gari babu burodin da za su sayawa yaransu. Bayan masu saya, yajin aikin ya shafi masu aiki a gidajen burodin da masu sayarwa a shaguna ko tallata shi. A Najeriya al'umma sun yi ittifaki babu yaran da gwamnati ke ji sai yajin aiki domin kawo sassauci ga abin da ke damun 'yan kasarta, musamman ma talakawa.