Wike da gwamnoni na kokarin ceto jam'iyyar adawa ta PDP
May 12, 2025Ministan Abuja Nyesom Wike da ake kai ruwa rana a kansa a jam'iyyar adawa ta PDP a karon farko ya halarci wani muhimmin taro na gwamnonin jam'iyyar a kokarin da suke yi na ceto PDP daga hali na koma baya da ma ficewar da 'ya'yanta ke yi zuwajam'iyyar APC mai mulki. Taron dai ya tsayar da ranar da zasu gudanar da taron majalisar zartaswar jamiyyar. Shin me halartar Wike taron ke nunawa a dai dai wannan lokaci da jam'iyyar ke cikin mawuyacin hali..
Jiga-jigan jam'iyyar adawa ta Najeriya ta PDP ne suka hallara a talatainin daren Litinin a Abujan a kokari na ceto jamiyyara daga halin da ta shiga tun bayan babban zaben da aka yi a 2023, inda guguwar masu ficewa daga jam'iyyar ya kara tada hankalin 'ya'yan nata. Duk da wannan girgiza da ta samu jam'iyyar wacce bata taba gani ba tun 1999 da ta kafa gwamnati a Najeriyar, shugaban jam'iyyar Ambassada Iliya Damagum ya ce sun hango mafita daga halin da suke ciki.
A karon farko ministan Abuja Nyesom Wike ya yi bayyana ban mamaki inda ya hallarci taron da aka yi, bayan kauracewa duk wasu taraurrukan jamiyyar da aka yi a baya na kusan shekaru biyu. Wike ya zama wanda ya fito fili yana sukan lamirin jamiyyar ta PDP inda ya yi tsayiwar gwamin jaki dayakafarsa a PDP sannan daya a APC. Shin me halartar Wike ke nunawa a wannan taro na jamiyyar ta PDP?
Taron na babbar jamiyyar adawa ta PDP a Najeriya ya kafa kwamiti mai mutane bakwai da zai shirya taron majalisar zartaswa na jam'iyyar da ake shirin gudanarwa a ranar 27 ga watan wanda zai share fagen babban taron jam'iyyar da za'a zabi sabbin shugabanin jam'iyyar da ya zame mata karfin kafa. Sanata Umar Ibrahim Tsauri dan majalisar gudanrawa ne na jamiyyar ta PDP da ya ce matakan da suka dauka ya na da tasiri.
Kaiwa ga tsayar da rana ta gudanar da taron majalisar zartaswa jam'iyyar da zai kai ga gudanar da babban taron PDP tamkar karya kwarin gwiwa da ya dade da harde jam'iyyar ce a kokari na mayar da mukamin shugabancinta ga shiyyar Arewa maso Tsakiyar Najeriyar don tunkarar zaben 2027 da tuni aka fara kada kugensa duk da cewa hukumar zabe bata dage haramci na yakin neman zabe ba.