SiyasaJamus
W.H.O. ta damu da bullar wasu cututtuka a Afirka ta Yamma
August 19, 2021Talla
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce yankin yammacin Afirka na fuskantar barazanar yaduwar cutukan Margurg da kuma Ebola, baya ga annobar corona da duniya ke fama da ita a yanzu.
Bullar sabbin cutukan biyu a yammacin na Afirka, ta kara fito da girman kalubalen da ke gaban gwamnatocin yankin a bangaren lafiya, tare da bukatar matakai ciki gaggawa.
Tuni ma dai kasar Ivory Coast ta fara yi wa jami'an lafiya alluran rigakafin cutar Ebola a farkon wannan makon.
Kuma a farkon makon ne hukumomi a Gini suka tabbatar da mutum na farko da cutar Marburg ta halaka a kasar.