WHO ta bukaci Trump ya dawo da bada agajin lafiya
March 17, 2025Shugaban Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi kira ga shugaban Amurka Donald Trump da ya duba matakin da ya dauka na dakatar da agajin da kasarsa ke baiwa kasashen duniya a fannonin lafiya.
Mista Ghebreyesus ya bayyana wannan matakin a matsayin wani mai barazana ga rayuwar miliyoyin al'umma da suka dogara da wannan agaji na Amurka.
Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban na hukumar lafiya ya ce matakin na Amurka ka iya mayar da hannun agogo baya a nasarar sama da shekaru 20 da aka cimma na yaki da cutar HIV AIDS a fadin duniya.
A watan da ya gabata ne, shugaban Amurkan ya sanar da dakatar da ayyukan hukumar dake bada agajin jinkai ta USAID, wacce aka samar sama da shekaru 60 da suka gabata. Kuma ya zuwa yanzu an soke kashi 83cikin dari na shirye shiryen hukumar.
Karin Bayani: Kasashen Afirka za su kawo karshen cutar Aids a tsakanin kananan yara