Isra'ila na aikata kisan kiyashi a Gaza
September 1, 2025Kashi 86 cikin 100 na mambobin kungiyar 500 da suka kada kuri'a sun goyi bayan kudurin, wanda ya ce "Manufofin Isra'ila da ayyukanta a Gaza sun kai matakin shari'a na kisan kare dangi.
Masananan sun ce bisa ga yarjejeniyar 1948 kan Rigakafi da hukuncin laifukan kisan kiyashi da aka cimma a zauren Majalisar Dinkin Duniya"
Har yanzu dai Isra'ila ba ta ce uffan ba game da wannan matakin da masanan suka cimma, wanda a baya kungiyar ta yi kakkausar suka kan cewa matakin Isra'ila a Gaza ka iya zama kisan kiyashi, sai da Isra'ilan ta ce tana kare kanta ne.
Isra'ila ta kaddamar da yakin Gaza bayan Hamas ta kai mata hari, inda ta kashe 'yan Isra'ila kusan 1,200 tare da kame 250
Yakin ya kashe mutane 63,000 a yankin Falasdinu a cewar ma'aikatar lafiya dake Gaza.
Karin Bayani:Dole ne Isra'ila ta yi sahihin bincike kan kisan mutum 20 a Gaza - MDD