Najeriya: Ko gwamnatin Tinubu ta yi nasara?
May 29, 2025Tun bayan karewar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2023, al'ummar Najeriya ke cike da fatan bayan hawan sabuwar gwamnati ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu za a samu sauye-sauye masu ma'ana a fannin ci-gaba talakawan kasar za su dara. To sai dai an samu akasin haka kuma gwamma jiya da yau, a cewar Ahmaed Abdullahi Yarima da ke zaman shugaban babbar jama'iyyar adawa a Najeriyar PDP na Unguwar Rogo da Ungwan Rimi cikin karamarhukumar Jos ta Arewa a jihar Plateau.
Gwamnatin APC dai na cewar ta samu nasarori da dama mussaman ta fuskar tattalin arziki da tsaro da yaki da cin-hanci da rashawa da ma kyautata hadin kan al'ummmar kasa, amma wata 'yar siyasa a jihar Plateau Madam Helen James na da ra'ayin cewa, har yanzu talakawan kasar ba su gani a kasa ba. Koda yake dai 'yan kasar sun ga yadda wasu'yan siyasa ke ribibin shiga jama'iyyar APC mai mulki a Najeriyar, a ra'ayin wani jigo a jam'iyyar adawar ta PDP a jihar Plateau din Dababa Aliyu masu yin hakan ba su da kishin talakawa. A cewarsa talakan Najeriya na ji a jikinsa, domin haka suna shirin kawar da gwamnatin a zaben shekara ta 2027. Yanzu haka dai shekaru biyu ne suka saura ga gwamnatin ta Tinubu ta kammala wa'adin mulkinta na farko, a dangane da haka lokaci ne zai nuna ko wata kila talakawan kasar za su ce madalla a sauran wa'adin wannan gwamnati ta APC.