Wani mutum ya kai hari da guduma kan matafiya a Jamus
July 3, 2025Wani mutum ya kai hari da guduma a cikin wani jirgin kasa a kudancin Jamus, inda ya jikkata mutane hudu kafin ‘yansanda su cafke shi, a cewar hukumomi.
Rundunar ‘yansanda ta bayyana cewa harin ya faru ne a cikin wani jirgin kasa mai gudun gaske na ICE, da ke kan hanyarsa daga birnin Hamburg na arewacin Jamus zuwa Vienna babban birnin Austria.
Maharin da ya kashe mutane a Solingen ya amsa laifinsa
Lamarin ya faru ne yayin da jirgin ke tsakanin garuruwan Straubing da Plattling a jihar Bavaria na Jamus.
A lokacin harin mutane kusan 500 ne ke cikin jirgin, in ji ‘yansanda kuma Kimanin jami'an tsaro 150 da ma'aikatan ceto da na kashe gobara aka tura zuwa wurin da lamarin ya faru.
Da farko, ‘yansanda sun ce wanda ya kai harin ya yi amfani da wani gatari, amma daga bisani ya koma amfani da guduma.
'Yansandan Jamus na farautar wani mahari
Hukumomi sun bayyana cewa dan asalin Syria mai shekaru 20 ne ake zargi da kai harin da ya raunata mutane hudu.