Wani jirgin ruwa ya kife a teku a Masar
July 3, 2025Talla
Kamfanin jirgin na ruwa wanda ke mallakin Saudiyya ne, ya tabbatar da mutuwar mutanen hudu, sannan ya ce ana zargin mutane uku sun bace.
Kamfanin dillancin labarai ta AP ya ambaci gwamnan lardin Bahar Maliyan a Masar, Amr Hanafy, yana cewa akwai ma'aikata 30 a cikin jirgin lokacin da ya yi kife.
Jiragen ruwa na rundunar sojin ruwa ta kasar Masar sun taimaka wajen gudanar da aikin ceto.
Har yanzu ba a bayyana dalilan da suka jawo wannan hadari ba, amma kafafen yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa jirgin na jan wani abu ne domin aikin hakar ma'adanai a wani wuri, a lokacin da ya kifen.