Manzon EU zai je Washington kan batun harajin Trump
July 16, 2025Babban jami'in da Hukumar Tarayyar Turai ta dorawa alhakin cimma yarjejeniya da Amurka kan karin harajin Donald Trump zai je birnin Washington a wannan Laraba, a kokarin samar da masalaha kan yakin kasuwanci da bangarorin biyu ke shirin tsundima.
Kwamishinan kasuwancin na EU Maros Sefcovic zai gana da takwarorinsa na gwamnatin Trump domin yi wa wannan tubka hanci, bayan da shugaban Amurka ya yi barazanar kara wa Tarayyar Turai haraji na kashi 30% daga ranar daya ga watan Agusta mai zuwa.
Karin bayani: Jamus ta ce dole EU ta dauki matakai kan karin harajin Trump muddin ba a samu masalaha ba
Shugaban na Amurka dai ya ce ya dauki wannan mataki ne saboda kasashen Turai da ci da gumin Washington a harkar cinikayya, yayin da ita ma EU ta dau alwashin ramawa kura aniyarta muddin ba su cimma daidaito ba.