Shin ko Kungiyar AES za ta dore?
February 7, 2025Kungiyar kasashen yankin Sahel ta AES da ta hada kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso na shirin daukar wani muhimmin mataki na samar da takardar Visa daya da ke ba da izinin shiga kasashen uku da aka kira da sunanVisa Liptako. An yi niya don saukaka zirga-zirgar jama'a cikin wannan yanki, wanda masu yawon bud ido, ko neman zuba jari iya amfani da wannan dama don biyan muradun su.
Kasashen na AES kuma za su yi amfani da tsarin diflomasiyya guda kan sauran batutuwa da suka rage a tattauna tsakanin kasashen uku da kungiyar da suka fice ta ECOWAS don samun masalaha.Shi daiwannan tsari na biza na Liptako, wani bangare ne na kokarin hada kai da kungiyar ta kasashen Sahel ke gudanarwa.
Wanda tun a a ranar 29 ga watan Janairu wadda takasance ranar ficewarsu daga ECOWAS , kasashen uku suka fitar da fasfo din su na AES a hukumance.
Sai dai a fuskar inganta zirga-zirgar jama'a a wannan yanki na AES, masana na ganin cewa akwai matakai na Zahiri da ta kamata wadannan kasashe su dauka muddin dai ana son mafaikin ya zamana gaskiya.
Sai dai duk da wannan matakai da ake magana a kan su, a hannu daya wani labari da ake kyautta zaton ya fito ne daga hukumomin Najeriya inda cibiyar ECOWAS take na cewa akwai wasu kasashe daga cikin kasashen na AES da suka yi tayin komawa cikin kungiyar ta ECOWAS.