Radiyo a karkara da sabuwar fasaha ta zamani
February 13, 2025Yayin da ake bikin ranar radiyo ta duniya mutanen karkara da galibi su sun dogara ne wajen samun sahihan labarai da bayanai ga kafofin watsa labaran na radiyo, musamman na kasashen ketare.
To amma kuma mutanen karkarar na bayyana kalubale da kuma matsalolin da suke cin karo da su kafin su iya sauraren labarai a yanzu sakamakon wasu sauye-sauyen zamani da ake samu ga kafofin watsa labarai,
Ashafa A. Dikko wani mazaunin kauyen Labani ne a cikin karamar hukumar Silame ta Jihar Sokwato:
‘'Idan ka auna nauyin kudin biyan caji kullum da kuma sayen data na saurare to karama sayen baturi duk da shi ma batur sai dai a ce Innalillahi wa Inna Ilaihi raji'un bisa yada kasarmu take ciki.
Ko da za a mayar da su takan waya ne kar a bar su ga babbar waya, a yi kokari a saka su ga kananan wayoyi yadda ba dole sai ka saka data ba, idan dai wayarka na da caji kana iya kamo tasha duk wadda ka ke so ka saurara''.
Shi kanshi yanayin sauye-sauye tattalin arziki da ke samu a duniya, wasu na cewa, ya kawo cikas da koma baya ga mutanen karkara, a kan yadda za su saurari gidajen rediyoyI na kasashen ketare idan aka kwatanta da inda aka fito.
Garba na Hali Kamba wani mazaunin karamar hukumar Kamba ta Jihar Kebbi ne:
‘'Akwatin radiyon kansa ya kara tsada, duba da shekarun baya karamin radiyo Kchibo bai wuce dari shida zuwa Naira dubu ba:
To yanzu sai ka sayi Kchibo karami mai kananan batur zai kai dubu takwas zuwa dubu goma. Mallakar babbar waya ga wanda ke cikin karkara wani babban aiki ne har ya yi tunanin saka mata data da caji, ita waya karama ma dole sai ka saye ta wajen dubu dari ko dubu dari da hamsin''.
Sannu a hankali dai wasu na ganin tasiri da kuma sauye-sauyen zamanin ga sauraren kafofin yada labarai, na iya sanya zamani ya dinka rigar da kowa zai iya kargamata, nan da wani dan lokaci.