Wagner zai dakatar da aiki a Mali
June 7, 2025Sojojin hayar Rasha na kamfanin nan na Wagner sun sanar da aniyarta ta barin kasar Mali, bayan kwashe sama da shekaru uku da rabi suna yakar masu ikirarin jihadi da ma wasu tsagerun da ke addabar jama'a a kasar.
Sai dai duk da sanarwar da kamfanin na Wagner ya fitar, Rasha za ta ci gaba da kasancewa da sojojinta na haya a yammacin Afirka.
Wata rundunar da ake kira The Africa Corps, ta fada a shafinta na Telegram a jiya Juma'a cewa ficewar Wagenr daga Mali ba za ta sauya komai ba dangane da kasancewar mayaka masu asali da Rasha a Malin.
Kasashen Mali da Burkina Faso da ma Jamhuriyar Nijar dai sun kwashe sama da shekaru 10 suna fama da mayakan tarzoma, cikinsu har da al-Qaeda da IS, inda Rasha ta yi alkawarin shigowa domin ba da nata taimako na yaki da 'yan ta'addar.