Von der Leyen na ziyara a Afirka
December 7, 2019Talla
Von der Leyen ta ambata hakan ne a wata ziyara da yanzu haka take yi a kasar Habasha inda ta zanta da shugaban Kungiyar AU Musa Faki Mahamat inda suka yi musayar yawu kan batutuwa da dama har ma suka amince su yi aiki tare wajen tinkarar matsala ta sauyin yanayi.
Baya ga shugaban AU da ta zanta da shi, Von der Leyen din har wa yau ta gana da firaministan Habasha Abiy Ahmed inda ya bukaci kungiyar ta EU da ta dafawa kasarsa wajen aikin da ta dauko na bunkasa tattalin arzkita.
Wannan dai ita ce ziyara ta farko da shugabar ta EU ta kai wata kasa da ba ta Turai ba tun bayan a ta fara jagorantar EU a ranar daya ga wannan watan da muke ciki.