Goma: Al'umma cikin mawuyacin hali
February 14, 2025Mai magana da yawun Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR Eujin Byun ta shaidawa manema labarai cewa, yakin da ake fafatawa a birnin Goma na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya tilasta kimanin mutane dubu 350 tserewa daga gidajensu tare da zama a filin Allah a yanzu haka.
A watan Janairun da ya gabata ne dai, kungiyar 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan makwabciyar kasa Ruwanda ta kwace iko da birnin Goma da ke zaman mafi girma a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon. Rahotanni sun nunar da cewa a yanzu haka kungiyar tawayen ta M23 na kutsa kai zuwa yankin kudancin Jamhuriyar Dimukuradiyyar ta Kwango, abin da mahukunta ke fargabar ka iya janyo tashin hankali na kan iyaka a yankin da dubban 'yan gudun hijira ke samun mafaka.