SiyasaUkraine
Ukraine ta zargi Rasha da saba alkawarin tsagaita wuta
April 20, 2025Talla
Gwamnatin Ukraine ta ce dakarun Rasha sun kai wasu jerin hare-hare da jirage marasa matuka a yankuna da dama na gabashin kasar, kazalika gwamnan Kherson, ya bayyana cewa an ji karar wasu manyan makamai a yankunan da dama a wannan Asabar, a yayin da ita kuwa rundunar tsaron Ukraine ta tabbatar da batakashi a tsaakanin dakarunta da na Rashar a fagen daga.
Daman tun daga farako, Shugaba Putin ne da kansa ya sanar da takaitaccen shirin na tsagaita wuta a albarkacin bikin Easter, don ba wa mabiya dama yin bukuwansu a cikin tsanaki, shelar da kuma gwamnatin Kiev ta sanar da za ta yi wa biyeyya kafin daga bisani batun ya sukurkuce.