Ukraine ta kakkabo gomman jiragen yakin Rasha
March 9, 2025Talla
Rundunar mayakan sama na kasar Ukraine ta ce ta kakkabo jiragen na Rasha guda 71 a yankunan kasar da Rashar ta hara cikin daren Asabar.
Sabon farmakin na Rasha sun kuma zo ne a yayin da Amurka ta sanarr da janye bai wa Ukraine din makaman yaki.
Ko a ranakun Juma'a da jiya Asabar ma dai hare-haren Rasha a gabashin kasar sun halaka mutum 14.
A ranar Talatar da ke tafe ne kuma ake sa ran hukumomin birnin Kyiv za su gana da masu shiga tsakani a Saudiyya, yayin Amurka ke kokarin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yakin na Rasha da Ukraine.