Ukraine ta kai hari kan cibiyoyin man Rasha
August 2, 2025Talla
Hukumomin Ukraine sun ce hare-haren sun yi sanadin tashin gobara a matatar man Ryazan da ke kusa da birnin Moscow. Sai dai Rasha ba ta mayar da martani kan harin ba. Ana ganin a yanzu Ukraine ta samu manyan makamai da ke cin dogon zango, ba kamar farko lokacin da Rasha ta mamaye kasar a shekarar 2022 ba.
Karin bayani: Ukraine ta kai farmaki kan jirgin yakin Rasha mafi girma
A gefe guda, ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar da kakkabo jirage marasa matuka 338 a cikin dare da Ukraine ta harba, yayin da ita Ukraine ta ce ta kakkabo 45 cikin 53 da Rasha ta harba su da nufin kai harin cikin dare. Rasha ta kuma ce ta karbe iko da wani kauye da ke gabashin Donetsk.