SiyasaAmurka
Ukraine ta amince da bukatar cinikin ma'adinai da Amurka
February 26, 2025Talla
Wani babban jami'i a gwamnatin Ukraine ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Amurka da Ukraine za su raba ribar da za a samu a cinikin ma'adinai da sauran albarkatun kasa da Allah ya hore wa Ukraine a wani mataki na bani gishiri na baka manda wajen shawo kan Washigton DC goyon bayan Kiev.
Karin bayani: Macron na neman shawo kan Trump game da rikicin Ukraine
Kazalika Ukraine za kuma ta bukaci tabbacin gudummuwar tsaro daga Amurka duk dai a kunshin daftarin da kasashen biyu za su sanyawa hannu. A makon da ya gabata ne Trump da Zelenskiy suka yi musayar kalamai a tsakaninsu kan mafarin takalar yakin Ukraine walau kaddara ko kuma ganganci.