Ukraine: Rasha ba ta da ta cewa kan Kiev
August 24, 2025Talla
Firaministan kanada Mark Carney ya ce Ukraine ce kadai da kawayenta suke da ikon yanke hukunci kan tabbacin tsaron kasar amma ba Rasha ba.
Ya baiyana haka ne yayin da Ukraine ta ke gudanar da zagayowar ranar samun yancin kan kasar.
Moscow da Kiev sun yi musayar fursunoni da suka hada da sojoji da fararen hula a yau Lahadi a mataki na baya bayan a musayar da suka fara a farkon wannan shekarar.
Bangarorin biyu sun yi musayar fursunoni 146 kowannensu.
Musayar fursunonin dai shi ne kadai cigaban da aka samu a matakan diflomasiyar da ake ta yi na samun daidai a tsakanin kasashen biyu tun bayan da rikici ya barke a tsakaninsu.