Ukraine da Rasha sun zargi juna da karya yarjejeniyar yaki
March 26, 2025Ukraine da Rasha sun zargi juna da karya yarjejeniyar dakatar da hare-hare kan rumbunan adana makamashi da Amurka ta jagoranci cimma wa, yayin da tarayyar Turai ke cewa ba za ta martaba sharuddan da Rasha ta gindaya kan janye harin Bahar Rum ba.
Karin bayani:Rasha ta ce da sauran tafiya kafin dakatar da yakin Ukraine
A ranar Talata Amurka ta sanar da cimma masalaha bayan tattauna daban-daban da Rasha da kuma Ukraine, don daina kai hari Bahar Rum da kuma cibiyoyin adana makamashin kasashen biyu.
Karin bayani:Trump zai tattauna da Putin don kawo karshen yaki a Ukraine
To sai dai shugaba Volodymyr Zelenskiy na Ukraine ya ce Amurka ta shaida masa cewa yarjejeniyar ta fara aiki ne nan take, wanda kuma fadar mulkin Rasha ta Kremlin ke cewa da sake kan batun kogin Bahar Rum, da ya raba nahiyar Turai da Asiya mai matukar muhimmanci.