SiyasaTurai
Ukraine da Rasha sun yi musayar fursunonin yaki 538
April 19, 2025Talla
Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunonin yaki na sama da mutum 500 kuma mafi girma tun bayan fara yaki a tsakanin kasashen biyu.
Karin bayani: Musayar fursunonin Rasha da Ukraine
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy, ya ce kasar sa ta karbi sojoji fursunonin yaki akalla 277 wadanda ke tsare a gidajen yarin Rasha, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Telegram.
Karin bayani: An mikawa Ukraine fursunonin yaki 1,200
Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta karbi sojojinta 246 daga Kiev, wadanda a halin yanzu ke kasar Belarus wacce ke kawance da Rasha kafin daga bisani a maida su gida. Kazalika hukumomin Moscow da Kiev sun jinjinawa UAE wajen gudanar da wannan gagarumin aiki cikin kwanciyar hankali.