Ukraine da Rasha sun amince da tsagaita wuta a Bahar Maliya
March 25, 2025Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa Rasha da Ukraine sun amince da daina amfani da tsinin bindiga a tekun Bahar Maliya domin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa tare da habaka kasuwanci. A cikin wasu bayanai biyu daban-daban da fadar mulki ta White House ta fitar bayan tattaunawa a Saudiyya da bangarorin da rikici da juna, Amurka ta ce a shirye take ta taimaka wa Moscow fitar da kayayyakin amfanin gona da taki zuwa kasuwannin duniya. Sannan Washington ta yi alkawarin taimaka wa Ukraine a kokarin da ake yi na musayar fursunoni, da sakin fararen hula da kuma mayar da 'yan Ukraine da aka tilasta wa gudun hijira gida.
Tuni dai shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana wannan mataki a matsayin "abu mai kyau" tare da alkwarin aiwatar da shi. Kazalika, Rasha da Ukraine sun amince da sanya wata hukuma ko kasa da za ta sa ido kan yarjejeniyar tsagaita bude wutar. Wannan dai, za ta bai wa Rasha damar fitar da kayayyakinta tare da inganta hanyoyin shiga tashar jiragen ruwa da tsarin biyan kudi na duniya. Amma dai Amurka ta yi alkawarin ci gaba da shirya tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine domin samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin sassa biyu.