SiyasaGabas ta Tsakiya
UAE za ta zuba jari na dala triliyan 1.4 a Amurka
May 15, 2025Talla
Shugaban kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa ya sanar da cewa kasarsa za ta zuba hannun jari na dala triliyan 1.4 a Amurka a tsawon shekaru 10 musamman a fannin kimiyya da fasahar kirkira ta AI da kuma makamashi.
Karin bayani:Trump a Gabas ta Tsakiya: Sulhu ko kasuwanci?
Wannan ce ziyararsa ta karshe a rangadin kwanaki hudu da yake yi a kasashen Gabas ta Tsakiya da suka hadar da Saudiyya da Qatar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.
Karin bayani: Trump na ziyara a kasashen Gabas ta Tsakiya
Gabanin ziyararsa Qatar da UAE Mr. Trump ya yi ganawar keke-da-keke da shugaban gwamnatin rikon kwaryar Siriya Ahmed al-Sharaa a birnin Riyadh wanda ya kai ga dage takunkumin da Amurka ta lafta wa Damascus na tsawon shekaru.