Turkiyya ta katse huldar kasuwanci da Isra'ila
August 31, 2025Talla
Turkiyya ta katse dukkan dangantakar kasuwanci da Isra'ila tare da rufe sararin samaniyarta ga jiragen Isra'ila, a matsayin martani kan abin da kasar ke yi a Zirin Gaza, in ji ministan harkokin wajen kasar, Hakan Fidan.
A zaman majalisar dokoki kan halin da ake ciki a Gaza da aka yi Ankara babban birnin kasar, Fidan ya bayyana cewa: sun rufe tashoshin jiragen ruwa ga Isra'ila, kamar yadda su ma jiragen ruwan Turkiyya za su daina zuwa tashoshin Isra'ila.
Kawo i yanzu dai babu wata kasa da ta dauki irin wannan mataki na datse huldar kasuwanci gaba daya da Isra'ila.
Tun bayan fara yakin Isra'ila a Gaza a farkon watan Oktoban 2023, sama da Falasdinawa dubu 62 ne aka kashe a rikicin, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas a yankin Falasdinu.