SiyasaTurkiyya
Turkiyya: An tsare lauyan Imamoglu
March 28, 2025Talla
Magajin garin Isantanbul Ekrem Imamoglu ya ce hukumomi sun kama lauyansa inda ake ci gaba da tsare shi.
Ya wallafa a shafinsa na X cewa an tsare lauyansa Mehmet Pehlivan bisa wasu dalilai da ba a fayyace ba.
Pehlivan ya wakilci Imamoglu a kotu a ranar lahadi kan zargin da ake yi masa na cin hanci.
Imamoglu ya kasance babban abokin hamaiyyar shugaba Recep Tayyip Erdogan, kuma an kama shi ne a makon da ya gabata yan sa'oi kafin ya baiyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa, lamarin da ya haifar da gagarumar zanga zanga da aka dade ba a gani ba a Turkiyya cikin shekaru goma da suka gabata.
Tun daga wannan lokaci hukumomin Turkiyya sun kama mutane kimanin 1,900 da suka hada da masu zanga zanga da kuma yan Jarida.