Turai ta nemi shugaban syriya ya sauka
July 18, 2011Ministocin ƙasashen Turai da ke kula da harkokin waje sun bukaci shugaba Bashar al-Assad na Syriya ya sauka daga karagar mulki, sakamakon gaza shawowa cikin ruwan sanyi rikicin ƙasarsa da ya ɓarke tun watanni huɗun da suka gabata. A lokacin wani taron haɗin guywa da ke gudana a wannan litinin a birnin Bruxelles na bejium, ministan harkokin wajen Suden ko Suede wato Carl Bildt ya bi sahun takwaran aikinsa na Birtaniya William Hague wajen bayyana cewar shugaba Assad ya zubar da mutuncinsa a idanun 'yan ƙasarsa da ma duniya baki ɗaya, biyowa bayan amfani da ƙarfin da ya ke yi domin murƙushe masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.
Ministocin suka ce ya zama wajibi walau shugaban na Syriya ya mutunta kiraye-kiraye garambawul da ake yi masa a harkokin mulki, ko kuma ya ya da ƙwallo domin ya rabu da ƙuda. Fararen hula kimanin 1 400 da kuma jami'an tsaro 400 ne aka tabbata cewar sun rasa rayukansu tun bayan ɓarkewar tashin hankali da kuma zub da jini a Syriya a watan maris. Ƙungiyar Gamayyar Turai ta ce ba za ta yi amfani da ƙarfi domin hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad ba. Amma kuma ministocin ƙasashenta 27 za su fitar da sanarwar haɗin guywa a wannan litinin game da sabbin matakan da Eu za ta ɗauka akan gwamnatin Syryia.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal