Ficewar tsohon shugaban Koriya ta Kudu daga fadar gwamnati
April 11, 2025A wannan Jumma'a tsohon Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol wanda aka tsige kuma kotun tsarin mulki ta tabbatar da matakin yake ficewa daga fadar gwamnati zuwa gidansa na kashin kansa, inda mutane suka yi dafifi magoya baya da masu adawa. Ranar Jumma'a da ta gabata kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da matakin majalisar dokoki na tsige tsohon shugaban saboda kakaba dokar ta-baci na soja da ya yi, abin da ya saba ka'ida.
Karin Baynai: Kotu ta amince da tsige shugaban Koriya ta Kudu
Yanzu haka za a gudanar da zaben shugaban kasa ranar 3 ga watan Yuni sai dai babu tabbas ko akwai wata rawar da tsohon shugaban Yoon Suk Yeol zai taka lokacin zaben mai zuwa.
A wani labarin kasar ta Koriya ta Kudu ta kulla huldar diplomasiyya da sabuwar gwamnatin Siriya.